DARASI NA 4: YADDA AKE ZAƁAR BATTERY MAI KYAU DON SOLAR
Gabatarwa Bayan mun san menene battery, yanzu za mu koyi yadda ake zaɓar battery mai kyau da ta dace da bukatarka.
DARASI NA 4: YADDA AKE ZAƁAR BATTERY MAI KYAU DON SOLAR
Gabatarwa
Bayan mun san menene battery, yanzu za mu koyi yadda ake zaɓar battery mai kyau da ta dace da bukatarka.
Abubuwan Da Ya Kamata A Duba
1. Ah (Ampere Hour)
Ah yana nuna yawan wutar da battery za ta iya adanawa.
Misali:
🔋 100Ah
🔋 150Ah
🔋 200Ah
Mafi girman Ah, mafi yawan wutar da za ta adana.
2. Voltage
Mafi yawan batirorin solar suna zuwa da:
✅ 12V
✅ 24V
✅ 48V
Ya kamata voltage ɗin battery ya dace da inverter ɗinka.
3. Nau'in Battery
Lead Acid
Gel Battery
Lithium Battery
Lithium tana da tsawon rai amma ta fi tsada.
4. Tsawon Rayuwa
Kafin ka saya, ka duba adadin shekarun da ake sa ran battery za ta yi aiki.
Shawara
✔ Ka sayi battery daga kamfani mai inganci.
✔ Ka tabbatar tana da garanti.
✔ Kada ka zaɓi battery saboda arha kawai.
Kammalawa
Zaɓin battery mai kyau yana taimakawa wajen samun ingantaccen aiki da kuma tsawon rayuwar solar system.
ZAKIN SOLAR NEWS ⚡ Karfi Daga Hasken Rana
What's Your Reaction?
Like
0
Dislike
0
Love
0
Funny
0
Angry
0
Sad
0
Wow
0