Lesson (1) gabatarwa akan koyon solar system
Menene Solar System? Solar system wata hanya ce ta samar da wutar lantarki ta amfani da hasken rana. Ana amfani da solar panel domin tara hasken rana sannan a maida shi wuta domin anfani a gida, shago ko office.
LESSON 1
GABATARWA AKAN SOLAR SYSTEM
Menene Solar System?
Solar system wata hanya ce ta samar da wutar lantarki ta amfani da hasken rana. Ana amfani da solar panel domin tara hasken rana sannan a maida shi wuta domin anfani a gida, shago ko office.
Solar system yana taimakawa wajen rage amfani da generator da NEPA.
MUHIMMAN KAYAN SOLAR SYSTEM
1. Solar Panel
Solar panel shine yake karɓar hasken rana ya maida shi wuta.
Aikinsa:
Tattara hasken rana
Samar da wutar DC
Nau’ikan Panel:
Monocrystalline
Polycrystalline
2. Battery
Battery tana ajiye wutar da panel ya samar domin anfani da ita da dare ko lokacin babu rana.
Nau’ikan Battery:
Dry battery
Gel battery
Lithium battery
3. Charge Controller
Wannan kayan yana kula da yadda wuta ke shiga battery.
Aikinsa:
Kare battery daga over charge
Kare battery daga lalacewa
Nau’ikan sa:
PWM
MPPT
4. Inverter
Inverter yana canza wutar DC zuwa AC domin anfani da kayan gida kamar:
Fan
TV
Fridge
Bulb
YADDA SOLAR SYSTEM KE AIKI
Solar panel yana tara hasken rana
Charge controller yana sarrafa wutar
Battery tana ajiye wutar
Inverter yana canza wutar zuwa AC
Sai ayi anfani da ita a gida
AMFANIN SOLAR SYSTEM
Rage kashe kuɗin fetur
Babu hayaniya kamar generator
Yana da tsabta
Yana aiki da rana da dare
Rage matsalar rashin wuta
KAMMALAWA
Solar system hanya ce mai sauƙi kuma mai anfani wajen samar da lantarki ta amfani da hasken rana. Fahimtar kayan solar shine matakin farko na koyon installation da gyaran solar system.
LESSON 1 END
ZAKIN SOLAR NEWS
“Karfi Daga Hasken Rana”
What's Your Reaction?
Like
1
Dislike
0
Love
0
Funny
0
Angry
0
Sad
0
Wow
0