LESSON 3 KOYON BATTERY A SOLAR SYSTEM
Menene Battery? Battery wata muhimmiyar na’ura ce a solar system wadda take ajiye wutar da solar panel ya samar domin anfani da ita idan babu rana ko da dare. Ba tare da battery ba, yawancin solar system ba zai iya bada wuta da dare ba.
LESSON 3
KOYON BATTERY A SOLAR SYSTEM
Menene Battery?
Battery wata muhimmiyar na’ura ce a solar system wadda take ajiye wutar da solar panel ya samar domin anfani da ita idan babu rana ko da dare.
Ba tare da battery ba, yawancin solar system ba zai iya bada wuta da dare ba.
AIKIN BATTERY
Battery tana:
✅ Ajiye wutar solar
✅ Bayar da wuta lokacin da ake bukata
✅ Taimakawa inverter yayi aiki
NAU’IKAN BATTERY
1. Dry Battery
Ita ce mafi amfani a solar system.
Fa’idarta:
✅ Tana ɗaukar lokaci
✅ Bata zubar da ruwa
✅ Bata da yawan matsala
Rashinta:
❌ Farashinta ya fi tsada
2. Gel Battery
Fa’idarta:
✅ Tana da ƙarfi
✅ Tana aiki sosai
Rashinta:
❌ Idan over charge yayi yawa tana iya lalacewa
3. Lithium Battery
Wannan ita ce sabuwar battery mai ƙarfi sosai.
Fa’idarta:
✅ Saurin caji
✅ Tana ɗaukar shekaru masu yawa
✅ Bata da nauyi sosai
Rashinta:
❌ Farashinta yana da tsada
YADDA AKE GANE KARFIN BATTERY
Ana auna battery da:
Voltage (V)
Ampere Hour (AH)
Misalai:
12V 100AH
12V 200AH
24V 200AH
MA’ANAR AH
AH yana nuna tsawon lokacin da battery zata iya bada wuta.
Misali:
100AH battery zata fi:
60AH
75AH
ƙarfin ajiye wuta.
ABUBUWAN DA KE LALATA BATTERY
❌ Over charge
❌ Rashin caji sosai
❌ Amfani da fake charger
❌ Zafi mai yawa
❌ Haɗa waya ba dai-dai ba
YADDA AKE KULA DA BATTERY
✅ A tabbatar da charge controller yana aiki
✅ Kada a bar battery ta mutu gaba ɗaya
✅ A ajiye ta a wuri mai iska
✅ A duba connection lokaci-lokaci
MUHIMMAN SHAWARA
Kada a haɗa inverter mai ƙarfin da yafi battery ƙarfi saboda yana iya rage rayuwar battery.
KAMMALAWA
Battery tana daga cikin muhimman kayan solar system saboda ita ce ke ajiye wuta domin anfani da ita a lokacin da babu rana. Fahimtar battery yana taimakawa wajen sanin yadda ake tsara solar system mai kyau.
LESSON 3 END
ZAKIN SOLAR NEWS
⚡ “Karfi Daga Hasken Rana”
What's Your Reaction?
Like
1
Dislike
0
Love
0
Funny
0
Angry
0
Sad
0
Wow
0