DARASI NA 5: MENENE INVERTER A SOLAR SYSTEM?
Gabatarwa A darussan da suka gabata mun koyi game da Solar Panel da Battery. Yanzu kuma za mu koyi game da Inverter, wanda yana daga cikin muhimman kayan solar system.
DARASI NA 5: MENENE INVERTER A SOLAR SYSTEM?
Gabatarwa
A darussan da suka gabata mun koyi game da Solar Panel da Battery. Yanzu kuma za mu koyi game da Inverter, wanda yana daga cikin muhimman kayan solar system.
Menene Inverter?
Inverter wata na'ura ce da ke canza wutar DC (Direct Current) da ke fitowa daga battery zuwa AC (Alternating Current) wadda kayan lantarki na gida ke amfani da ita.
Aikin Inverter
✅ Canza wutar DC zuwa AC.
✅ Samar da wuta ga TV, Fan, Firiji da sauran kayan lantarki.
✅ Taimakawa wajen gudanar da kayan gida cikin sauƙi.
Nau'ikan Inverter
1. Pure Sine Wave Inverter
Yana bada wuta mai inganci sosai.
Ya dace da TV, Fridge, Computer da sauran kayan lantarki masu tsada.
2. Modified Sine Wave Inverter
Farashinsa ya fi sauƙi.
Bai kai Pure Sine Wave inganci ba.
Yadda Ake Auna Inverter
Ana auna inverter da:
🔹 1KVA
🔹 2.5KVA
🔹 3.5KVA
🔹 5KVA
🔹 10KVA
Mafi girman KVA, mafi yawan kayan da zai iya ɗauka.
Abubuwan Da Ya Kamata A Lura Da Su
✔ Ka zaɓi inverter da ya dace da yawan kayan da kake son amfani da su.
✔ Ka tabbatar battery da inverter sun dace da juna.
✔ Ka guji ɗora masa kayan da suka fi ƙarfinsa.
Kammalawa
Inverter shi ne zuciyar amfani da wutar solar a gida, domin shi ne ke canza wutar battery zuwa wutar da kayan lantarki ke amfani da ita.
Darasi Na Gaba:
Lesson 6: Menene Charge Controller Kuma Menene Aikinsa?
What's Your Reaction?
Like
0
Dislike
0
Love
0
Funny
0
Angry
0
Sad
0
Wow
0