LESSON 2 KOYON SOLAR PANEL

Menene Solar Panel? Solar panel shine mafi muhimmancin kayan solar system. Shi ne yake karɓar hasken rana ya maida shi wutar lantarki domin anfani a gida ko office.

May 28, 2026 - 14:11
May 30, 2026 - 19:19
 0  19
LESSON 2 KOYON SOLAR PANEL

LESSON 2

KOYON SOLAR PANEL

Menene Solar Panel?

Solar panel shine mafi muhimmancin kayan solar system. Shi ne yake karɓar hasken rana ya maida shi wutar lantarki domin anfani a gida ko office.

Ana haɗa solar panel da:

Battery

Charge Controller

Inverter

Domin samar da cikakken tsarin solar.

YADDA SOLAR PANEL KE AIKI

Lokacin da rana ta haska panel:

Panel yana karɓar hasken rana

Sai ya maida hasken zuwa wutar DC

Wutar zata shiga charge controller

Daga nan battery zata ajiye wutar

Inverter zai canza ta zuwa AC

NAU’IKAN SOLAR PANEL

1. Monocrystalline Panel

Wannan shine mafi ƙarfi kuma mafi inganci.

Fa’idarsa:

✅ Yana saurin cika battery

✅ Yana aiki sosai ko da rana bata yi ƙarfi ba

✅ Yana ɗaukar lokaci mai tsawo

Rashinsa:

❌ Farashinsa ya fi tsada

2. Polycrystalline Panel

Shi ma yana aiki sosai amma bai kai mono ƙarfi ba.

Fa’idarsa:

✅ Farashinsa ya fi sauƙi

✅ Yana da kyau ga ƙananan system

Rashinsa:

❌ Bai da ƙarfi sosai idan rana bata yi kyau ba

YADDA AKE GANE PANEL MAI KYAU

Abubuwan dubawa:

✅ Watts na panel

✅ Voltage

✅ Original ko fake

✅ Girman panel

✅ Warranty

MISALIN WATTS NA PANEL

100W Panel

200W Panel

300W Panel

550W Panel

Mafi yawan watts yana bada ƙarin wuta.

ABUBUWAN DA PANEL ZAI IYA JA

Misali:

200W Panel:

Zai iya:

Cajin battery

Kunna bulb

Fan

TV

550W Panel:

Zai iya bada wuta mai yawa ga:

Freezer

Inverter

Gida mai ɗan girma

YADDA AKE KULA DA PANEL

✅ A rika goge kura

✅ Kada inuwa ta rufe shi

✅ A girka shi inda rana ke haskawa sosai

✅ A tabbatar da waya tayi kyau

MUHIMMAN SHAWARA

Kada a haɗa panel kai tsaye da battery ba tare da charge controller ba domin yana iya lalata battery.

KAMMALAWA

Solar panel shine zuciyar solar system saboda shine yake samar da wutar farko daga hasken rana. Fahimtar yadda yake aiki yana taimakawa wajen sanin installation da gyaran solar system.

LESSON 2 END

ZAKIN SOLAR NEWS

⚡ “Karfi Daga Hasken Rana

What's Your Reaction?

Like Like 1
Dislike Dislike 0
Love Love 0
Funny Funny 0
Angry Angry 0
Sad Sad 0
Wow Wow 0