Gawuna Ya Yi Watsi Da Tayin Kujerar Mataimakin Gwamna Da Sanata

An ruwaito cewa tsohon ɗan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna, ya yi watsi da tayin da ake zargin jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi masa.

May 28, 2026 - 13:24
May 28, 2026 - 13:26
 0  8
Gawuna Ya Yi Watsi Da Tayin Kujerar Mataimakin Gwamna Da Sanata

Gawuna Ya Yi Watsi Da Tayin Kujerar Mataimakin Gwamna Da Sanata — Rahoto

An ruwaito cewa tsohon ɗan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna, ya yi watsi da tayin da ake zargin jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi masa.

Rahotanni sun bayyana cewa tayin ya haɗa da kujerar mataimakin gwamna ko kuma takarar Sanatan Kano ta Tsakiya domin samar da haɗin kai a siyasar Kano gabanin zaɓen shekarar 2027.

Sai dai wata majiya ta bayyana cewa Gawuna bai amince da tayin ba, yana mai cewa ya shiga tafiyar siyasa ne ba tare da wani sharadi ba, kuma zai ci gaba da kasancewa a cikinta.

Jaridar Daily Nigerian ta ce Gawuna ya nuna cewa biyayyarsa da tafiyarsa ta siyasa ba ta dogara da neman mukami ba.

What's Your Reaction?

Like Like 0
Dislike Dislike 0
Love Love 0
Funny Funny 0
Angry Angry 0
Sad Sad 0
Wow Wow 0