Saniya Mai Kama Da Donald Trump Ta Tsallake Layya A Bangladesh

Wata saniya da ta shahara a kafafen sada zumunta saboda irin gashin kanta mai launin ruwan zinariya, wadda aka yi wa laƙabi da “Donald Trump”, ta tsallake yankawa a bikin Babbar Sallah a ƙasar Bangladesh bayan gwamnatin ƙasar ta shiga tsakani.

May 28, 2026 - 15:41
 0  7
Saniya Mai Kama Da Donald Trump Ta Tsallake Layya A Bangladesh

Wata saniya da aka yi wa laƙabi da “Donald Trump” saboda irin gashin kanta mai launin ruwan zinariya, ta tsallake yankawa a bikin Babbar Sallah a ƙasar Bangladesh bayan gwamnatin ƙasar ta shiga tsakani.

Sanarwar jami’an ma’aikatar harkokin cikin gidan ƙasar ta ce an riga an sayar da saniyar domin yin layya, amma gwamnati ta dakatar da hakan bayan yadda ta shahara a kafafen sada zumunta tare da jawo taron jama’a daga wurare daban-daban.

Saniyar, wadda aka bayyana a matsayin wata nau’in saniya farar fata mai wuya a samu a Bangladesh, tana da nauyin kusan kilo 700, kuma ta shahara ne saboda gashin kanta da mutane suka ce yana kama da salon gashin shugaban Amurka, Donald Trump.

Mai gonar da ake kiwon saniyar, Ziauddin Mridha, ya ce ƙanensa ne ya fara kiranta da “Donald Trump” bayan ya lura da kamanninta.

Ya kuma bayyana cewa saniyar tana da natsuwa sosai kuma tana buƙatar kulawa ta musamman ciki har da yawaita ciyarwa da wanka akai-akai.

Gwamnatin Bangladesh ta mayar da saniyar zuwa babban gidan namun daji na ƙasar da ke Dhaka, bayan da aka mayar wa wanda ya saya kuɗinsa.

What's Your Reaction?

Like Like 1
Dislike Dislike 0
Love Love 0
Funny Funny 0
Angry Angry 0
Sad Sad 0
Wow Wow 0